Adadin mutanen da cutar coronavirus ta kashe a Italia ya zarce 230
Gwamnatin Kasar Italia tace adadin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus ya kai 233 sakamakon karin mutane 36 da suka mutu, yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar ya tashi daga 1,247 zuwa 5,883.
Wallafawa ranar:
Alkaluman da hukumomi suka bayar sun nuna cewar yanzu haka mutanen dake cikin mawuyacin hali a asibiti ya kai 567 daga cikin 462 da ake da su a jiya juma’a.
Ya zuwa yanzu an samu masu dauke da cutar a kowanne yanki na yankunan kasar 22, abinda ya tada hankalin gwamnati.
Jami’an agajin gaggawa sun bayyana cewar yanzu haka ana fama da karancin gadajen asibiti a Yankin Lombardy dake kusa da Milan.
Italia ce kasa ta farko da aka fi samun wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar bayan China, kuma itace ta 3 da aka fi samun masu dauke da cutar bayan China da Koriya ta Kudu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu