Saudiya

Saudi Arabia ta tsare 3 daga cikin manyan ‘yan gidan sarautar kasar

Yerima mai jiran gado na Saudiya Mohammed bin Salman.
Yerima mai jiran gado na Saudiya Mohammed bin Salman. Mandel Ngan/Pool via REUTERS/File Photo

Hukumomin Saudi Arabia sun kama 3 daga cikin manyan ‘yan gidan Sarautar kasar cikin su harda ‘dan uwan Sarki Salman bin Abdulaziz wato Yarima Ahmad bin Abdulaziz. Cikin wadanda aka tsare sun hada da Yarima Ahmed Bin Abdulaziz da Yarima Mohammed bin Nayef, wanda shine mai jiran gado kafin Sarki salman ya tube shi ya kuma nada dan sa, sai kuma Yarima Nawaf bin Nayef.

Talla

Rahotanni sun ce daukar matakin tsare wadannan mutane na daga cikin shirin Yarima Mohammed bin Salman na karfafa karfin fada aji ganin tasirin mutanen da aka tsare.

A shekara ta 2017 ne aka kaffa wani kwamitin yaki da cin hanci da rashawa, a karkashin shugabancin yarima Mohammed Ben Salmane mai shekaru 32 a lokacin.

Yan lokuta da sanar da kaffa wannan kwamitin a lokacin,tashar talabijen Al Arabiya dake karkashin masarautar kasar ta sanar da kama wasu yarimomi 11 ,ministoci 4 da wasu tsofin mutane da suka taba rike mukamai.

Wata majiya daga kasar ta sheidawa kamfanin dilanci labaren faransa na Afp cewa hukumomin na Saudiya sun haramtawa wasu jiragen sama na wasu atajiran kasar cirawa ,wata hanyar hana su tserewa daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.