Duniya

An gudanar da bukukuwan ranar mata a Asia

Wasu daga cikin mata dake gudanar da  zanga-zanga  a Uruguay dangane da ranar Mata ta Duniya
Wasu daga cikin mata dake gudanar da zanga-zanga a Uruguay dangane da ranar Mata ta Duniya Miguel ROJO / AFP

Dubban Mata ne suka yi tattaki a kasashen Asia domin gudanar da bikin ranar mata ta duniya duk da barazanar cutar coronavirus wadda ke cigaba da hallaka rayuka.A kasar China inda cutar tafi illa wajen kashe mutane sama da 3,500 da kuma kama mutane sama da 100,000 a fadin duniya, tashar talabijin din kasar tayi rahoto na musamman kan gudumawar da mata ke bayar wa wajen kula da masu dauke da cutar.

Talla

Duk da barazanar cutar an gudanar da gangami a kasashen Thailand da Indonesia da Philippines da kuma Pakistan inda matan su bukaci basu ‘yanci.

An soke wani shirin tseren yada kanin wani a India yayin da Firaminista Narendra Modi ya baiwa wasu fitattun mata kafofin sa na sada zumunta domin gudanar da su saboda bikin na yau.

A kasar koriya ta kudu ma an soke bukukuwan saboda yaduwar cutar COVID-19 da ta kama mutane sama da 7,000, yayin da a Bangkok matan sun kayi gangami wajen neman Karin gurabun aiki.

A Manila dake Philippines daruruwan mata ne suka yi gangami tare da maza inda suka kona mutum mutumin shugaba Rodrigo Duterte wanda suka zarga da cin zarafin mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI