Turai

Ministan wasannin Italia ya bukaci dakatar da wasannin Serie A

Ministan wasannin Italia Vincenzo Spadafora ya bukaci soke daukacin wasannin gasar kwallon kafar Seria A da ake shirin gudanarwa yau saboda yaduwar cutar coronavirus wadda ta kashe mutane 233 a cikin kasar

Fafatawa tsakanin Juventus da AC Milan a gasar Serie A na kasar Italiya
Fafatawa tsakanin Juventus da AC Milan a gasar Serie A na kasar Italiya Yahoosports
Talla

A sakon da ya aikewa shugabannin hukumar kwallon kafar Italia, ministan yace rashin hankali ne a cigaba da gudanarwa da wasannin bayan sun bukaci daukacin mutane su zauna cikin gidajen su domin dakile yada cutar.

Ministan yace cigaba da gudanar da wasannin zai jefa rayuwar ‘Yan wasa da alkalai da masu horar da ‘yan wasa da su ma ‘yan kallo cikin hadari.

Ko a makon jiya sanda aka soke wasu wasannin domin kaucewa yaduwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI