Turai

Faransawa na nuna fargaba dangane da Coronavirus

Shugaban Faransa EmmanuelMacron ya ziyarci  asibitin dake kula da mutane da suka kamu da Coronavirus
Shugaban Faransa EmmanuelMacron ya ziyarci asibitin dake kula da mutane da suka kamu da Coronavirus Ludovic Marin/Pool via REUTERS

Hukumomi a Faransa na cikin shiri a kokarin su na yakar cutar Coronavirus, inda yanzu haka alkaluma suka bayyana cewa mutane 33 ne suka mutu daga cikin wandada suka kamu da ita.Yan kasar na ci gaba da bayyana damuwa a dai dailokacin da ya rage kwanaki hudu a gudanar da zaben kananan hukumomi.

Talla

Bayan bulluwar cutar Coronavirus a watan Disemba na shekara da ta shude akalla mutane 4300 ne suka mutu daga cikin mutane dubu 119.711 da aka gano sun kamu da cutar.

Faransa kasa ta biyu a Turai bayan kasar Italiya da cutar ta fi muni, Jean Francois Delfraissy shugaban hukumar wayar da kawuna na kasar ya bayyana cewa da sauren aiki a gaban su yanzu haka.

Daga cikin mutane 1.784 da ssuka kamu da cutar,33 ne suka mutu, Gwamnatin kasar ta shirya tsap wajen daukar matakan da suka dace domin hana yaduwar wannan cuta ,duk da cewa wasu rahotanni na tabbatar da cewa cutar za ta kai wani matsayi na anoba, ba tareda hukumomi sun sanar da haka ba, gani cewa za a gudanar da zaben wakilan kananan hukumomin da na magadiyan gari a Faransa.

Yaduwar coronavirus a Faransa ya kai wani matsayi bayan da aka tabbatar da cewa daya daga cikin ministocin kasar ya kamu da ita, gwamnati na daf da bayyana cutar a matsayin anoba a cewar wasu majiyoyi daga fadar Shugaban kasar .

Alamar tambaya ,yanzu duk da yake cutar ta saka shaku a zukatan Faransawa,ko za su fito ranar zaben domin kada kuri’u su kasancewar an hana gangami jama’a,hanyar da aka gano cewa an fi gaggawar kamuwa da coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.