Faransa

Faransa ta bada umurnin rufe makarantu saboda cutar corona

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Elysee

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bada umurnin rufe makarantun kasar saboda dakile yaduwar cutar coronavirus, yayin da ya bukaci masu shekaru sama da 70 da su zauna cikin gidajen su.

Talla

A jawabin da ya yiwa al’ummar kasar dangane da cutar da ta kasea mutane 61 a Faransa da kuma kama mutane kusan 2,900, Macron yace ya zama dole a dauki kwararan matakai domin dakatar da cigaba da yaduwar ta.

Shugaban yace daga ranar litinin mai zuwa za’a rufe makarantu da jami’oin kasar har sai abinda hali yayi nan gaba, yayin da ya bayyana cewar za’a cigaba da shirin gudanar da zaben majalisun kananan hukumomi a karshen wannan mako.

Majalisun kananan hukumomi sun bayyana daukar matakan kariya ga masu zuwa kada kuri’u ciki harda samar musu abinda zasu tsaftace hannayen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.