Manajan kungiyar Arsenal Mikel Arteta ya kamu da coronavirus
Wallafawa ranar:
Manajan kungiyar kwallon kafar Arsenal dake London Mikel Arteta ya kamu da cutar coronavirus wadda ke cigaba da lakume rayuka a kasashen duniya, abinda ya sa aka soke karawar da kungiyar sa zata yi da Brighton gobe asabar.
Arteta ya bayyana bakin cikin sa da matakin, bayan gwajin da yayi wanda ya tabbatar da cewar ya kamu da cutar.
Kungiyar Arsenal ta rufe filin wasan ta sakamakon kamuwar manajan, yayin da aka umurci wadanda suka yi mu’amala da Arteta da su killace kan su.
Babban daraktan kungiyar Arsenal Vinai Vankatesham ya bayyana halin lafiyar jama’ar su a matsayin abinda yafi muhimmanci.
Dan wasan Chelsea Callum Hodson-Odoi shine an farko a gasar Firimiya da ya kamu da cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu