Turai

Yau kasar Girka zata rantsar da shugabar kasa mace ta farko

Ekaterini Sakellaropoulou mace ta farko Shugabar kasar Girka
Ekaterini Sakellaropoulou mace ta farko Shugabar kasar Girka AFP/Eurokinissi/Vassilis Rempapis

Yau Girka zata rantsar da mace ta farko a matsayin shugabar kasa a tarihin kasar, a daidai lokacin da ta ke fama da matsalar cutar coronavirus ko kuma COVID-19.Ana saran Ekaterini Sakellaropoulou mai shekaru 63 wadda ke cikin manyan alkalan kasar ta sha rantsuwar kama aiki na shekaru 5 a Majalisa kafin daga bisani ta aje firanni a wajen da ake bikin tunawa da mazan jiya.

Talla

Yan Majalisun kasar 261 suka zabe ta daga cikin su 300 dake zauren majalisa ba tare da nuna banbancin siyasa ba.

Sakellaropoulou ta bayyana batutuwan da zata sanya a gaba da suka hada da tinkarar matsalar tattalin arziki da sauyin yanayi da kuma matsalar bakin dake kwarara zuwa kasar.

Sabuwar shugabar ce mace ta farko da ta jagoranci alkalan kotun kasa kuma mahaifin ta alkalin kotun koli ne.

Duk da yake Firaminista ne ke jagorancin harkokin gwamnati, shugaban kasa a Girka wanda na jeka nayi ka ne ke da hurumin amincewa da gwamnati da sanya kasa zuwa yaki tare da amincewar gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.