Amurka

Donald Trump ya amince a gudanar da gwaji a kan sa

Shugaban Amura a bikin cin abinci da tawagar Brazil a Palm Beach da Shugaban Brazil Jair Bolsonaro
Shugaban Amura a bikin cin abinci da tawagar Brazil a Palm Beach da Shugaban Brazil Jair Bolsonaro REUTERS/Tom Brenner

Shugaban Amurka Donald Trump ya amince a gudanar da gwaji a kan sa dangane da cutar Coronavirus,indan aka yi tuni Donald Trump ya bayana adawar sa tsawon dogon lokaci ga bukatar jami’an kiwon lafiya da suka bukaci gudanar da wannan gwaji don tabbatar da cewa ba shi dauke da kwayar cutar Coronavirus.

Talla

A jawabin likitan dake kula da lafiyar Shugaban Amurka Sean Conley Shugaba Donald Trump bashi dauke da kwayar cutar Coronavirus,wanda aka share wani lokaci ana cece kutse a kai bayan bikin cin abinci da yayi da wata tawagar kasar Brazil a Florida.

Shugaban Amurka mai shekaru 73 da kan sa ne ya bayyana cewa ya amince a gudanar da gwaji  domin kawar da jita-jita da ake a kai.

Amurka ta sanar da daukar matakan hana yaduwar cutar a kasar da kuma dakatar da jigilar jama'a zuwa wasu kasashe dama shiga Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.