Faransa

Faransa ta tsawaita batun killace yan kasar

Edouard Philippe a lokacin da yake sanar da karin kwanaki dangane da batun killacxe Faransawa
Edouard Philippe a lokacin da yake sanar da karin kwanaki dangane da batun killacxe Faransawa Christophe Ena / Pool via REUTERS

Gwamanatin Faransa ta sanar da kara wa’adin kwanaki dangane da batun killace yan kasar zuwa 15 ga watan Afrilu mai kamawa. Sanarwar dake zuwa bayan da Franministan Faransa Edouard Philippe yayi gargadi dangane da tsanantar annobar coronavirus a kasar, inda yace lamarin na iya zarta hakan kwanaki masu zuwa.

Talla

Hukumomin Faransa na ci gaba da yin gargadi gay an kasar don ganin sun yi amfani da matakan kariya daga kamuwa da cutar Coronavirus, gwamnatin kasar ta umurci sojoji wajen bayar da nasu goyan baya ga jami’an kiwon lafiya a yaki da Coronavirus.

Wannan na zuwa ne bayan da mutane sama da 365 suka mutu yayin da wasu 2300 suka kamu da cutar a kasa da sa’o’i 24 a kasar, asibitoci a Faransa na karancin gadaje saboda yawan masu dauke da cutar yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.