Turai

Matar Firaministan Canada ta warke daga Coranavirus

Firaministan Canada  Justin Trudeau da  mai dakin sa Sophie Gregoire Trudeau
Firaministan Canada Justin Trudeau da mai dakin sa Sophie Gregoire Trudeau REUTERS/Carlo Allegri

Mai dakin Firaministan Canada Justin Trudeau a jiya asabar ta sanar da warkewa daga kamuwa da coronavirus, annobar da ta tilastawa Firaministan kasar killace kan sa tsawon makonni biyu.

Talla

Ranar 12 ga watan Maris aka tabbatar da cewa maidakin Firaministan Canada na dauke da cutar Coronavirus wacce ta kuma bi umurnin jami’an kiwon lafiya da suka taimaka aka cimma wannan nasara.

A baya dai Firaministan kasar Justin Trudeau da babbar murya ya sanar da yan kasar cewa ya kamu da cutar ,sabili da haka killace kan sa ne ya fi zama alheri.

Ana ci gaba da sa ran gani jama’a sun bi umurnin jami’an kiwon lafiya don kawar da wannan annobva daga doron Duniya .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI