Wasanni-Kwallon kafa

Brazil ta janye daga shirya gasar cin kofin Duniya na mata a shekara ta 2023

Tambarin hukumar kwallon kafa na Duniya Fifa
Tambarin hukumar kwallon kafa na Duniya Fifa Reuters

Gwamnatin kasar Brazil, ta yi watsi da bukatar shirya gasar cin kofin kwallon kafa na Duniya na mata a shekara ta 2023.Gwamnatin kasar ta bayyana cewa, ganin matsakaicin yanayi tattalin arziki da kasar ke fuskanta bayan bulluwar annobar Covid 19,ba za ta iya baiwa hukumar kwallon kafa ta Duniya Fifa tabbacin cewa ta na a shirye don karbar wannan ganggami na Duniya.

Talla

Bayan janyewar kasar ta Brazil yanzu haka ya rage kasashen Colombia, Japan da kasashen Austria da New Zeland daga cikin layin masu neman wannan kujera.

Ranar 25 ga wannan watan da muke cikin sa ne ake sa ran hukumar Fifa ta fitar da sunan kasar da zata shirya gasar cin kofin Duniya na mata na shekara ta 2023.

A gasar cin kofin Duniya ta mata da ta gudana Faransa, Faransa ce ta fitar da kungiyar Brazil ,tun wannan lokaci ne hukumar kwallon kafar ta Brazil ta nada yar kasar Sweden Pia Sundhage a matsayin mai horar da kungiyar ta Brazil,

Janyewar Brazil ba a bin mamaki bane, ganin cewa kasar na jerrin kasashe da ke fama da annobar Covid 19 inda aka samu kusan mutuwar mutane dubu 37,banda haka bamkin Duniya na hasashen cewa tattalin arzikin kasar zai fuskanci koma baya na kusan kashi 8 cikin dari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI