Faransa

Faransawa sun nuna goyan baya ga iyalan Floyd

Dubban Mutane suka karrama George Floyd a birnin Paris dake Faransa, yayin da Firaminista Edouard Philippe ya sake jaddada cewar kasar da jami’an tsaron ta basa nuna irin wancan banbancin launin fatar sakamakon korafin jama’a.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Paris na kasar Faransa
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Paris na kasar Faransa REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Wasu daga cikin wadanda suka halarci inda aka karrama Floyd a Paris na kasar ta Faransa sun dauki allunan dake dauke da rubuce rubuce ciki harda zargin yan Sandan Faransa da aikata irin wancan laifi.

Sai dai Firaminista Philippe ya bayyana yan Sandan Faransa da Jandarmeri a matsayin wadanda basa nuna wariyar launin fata.

A cikin wannan makon ne Shugaban kasar Emmanuel Macron ya bukaci gwamnatin kasar ta gaggauta daukar matakai da za su kai ga samar da tsare-tsare don inganta aikin dan Sanda a Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI