Hadarin Tankin mai ya hallaka mutane a China
Wallafawa ranar:
Wani Hadarin tankin mai a China yayi sanadiyar hallaka mutane 10 da kuma jikkata wasu 117 lokacin da motar ta kama da wuta ta kuma tarwatse.Rahotanni sun ce karfin fashewar da ta yi ya sa wutar ta kama gidajen jama’a da motoci da kuma kamfanoni, abinda ya haifar da mummunar gobara da hayaki wanda ya tirnike sararin samaniya.
Bidiyon hadarin da aka yada ta kafar sada zumunta ya nuna yadda wutar tayi karfi sosai a kusa da birnin Wenling dake gabashin Yankin Zhejiang.
Masu aikin agaji na can suna kai dauki ga wadanda gobarar da ritsa da su, yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane 10 da kuma jikatar wasu 117.
Hukumomin yankin na ci gaba da kira ga jama'a da su kauracewa wasu daga cikin unguwani da lamari ya faru, ake kuma kyautata zaton wuta za ta yi barna a kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu