Faransa

Yan Sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Faransa

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a birnin Paris na kasar Faransa
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a birnin Paris na kasar Faransa REUTERS/Benoit Tessier

Kusan mutane dubu uku ne  yau suka yi gangami a kasar Faransa domin nuna bacin ransu da wariyar jinsi da kuma yadda Yan Sanda ke cin zarafin jama’a sakamakon kisan gillar da aka yiwa Adama Traore  bakar fata a watan yulin shekarar 2016 a Paris.

Talla

Rahotanni sun ce dubban mutane suka yi gangami a tsakiyar birnin Paris  da wasu biranen kasar ta Faransa domin amsa kirar da masu shirya zanga zangar dake wakiltar bakar fata Adama Traore da Yan Sanda suka kashe lokacin da yake hannun su a shekarar 2016.

Gangamin na zuwa ne lokacin da hukumar dake sa ido a harkokin Yan Sanda tace ta karbi korafe korafe kusan 1,500 kan yadda Yan Sandan ke cin zarafin jama’a.

Yar uwar Traore, Assa ta bukaci mahalarta gangamin da su yi Allah wadai da kin yiwa jama’a adalci da kuma cin zarafin da jami’an Yan Sandan keyi tare da bukatar ganin an gudanar da bincike kan yadda aka kashe dan uwan ta.

Assa tace kisan George Floyd a Amurka yayi daidai da yadda aka kashe dan uwan ta a Faransa, yayin da masu halartar gangami ke dauke da kyalen dake da rubuce rubucen neman yiwa Adama Traore adalci.

A wasu biranen kasar ta Faransa yan Sanda sun yi amfani da barkon tsofuwa wajen tarwatsa masu zanga-zanga,inda ofishin Ministan cikin gidan kasar ya bayyana yawan masu zanga-zangar da kusan dubu uku.

Gobe ake saran shugaba Emmanuel Macron zai yiwa al’ummar kasar jawabi kan shirin sakin mara sakamakon killace jama’ar kasar da akayi saboda yaki da cutar coronavirus, kuma ana saran zai tabo batun cin zarafin Yan Sanda cikin jawabin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI