France

Faransa zata bude harakokin kasuwanci

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron franceinfo

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yace kasar ta samu nasarar farko kan annobar coronavirus duk da yake ba’a kamala fafatawa ba a tsakanin su ganin irin illar da cutar ta yiwa kasar.

Talla

Yayinda yakegabatar da jawabin sa zuwa al’ummar kasar Macron yace yana farin cikin nasarar da suka samu wanda zai bada damar bude harakokin kasuwanci da suka shafi shagunan sayar da abinci da wuraren shan kofi daga wannan litinin.

Shugaban yace za’a rage darajar girman annobar a yankunan Faransa cikin su harda birnin Paris, yayin da ya bayyana matsayin kasar na yaki da wariyar launin fata da kuma cin zarafin jama’a, duk da yake shugaban yace ba zasu shafe wani sashe na tarihin kasar wajen kawar da wasu gine gine dake da nasaba da hakan ba.

Macron yace Faransa ba zata shafe tarihi ko sunan wani dake da nasaba da tarihin ta ba, kuma ba zasu manta da abinda ya faru ba ko kawar da wani mutum mutumi ko sunan dake da nasaba da abinda ya faru ada ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI