Asiya

An daure yar jarida a Philippines

Wata Kotu a Philippines ta yanke hukuncin dauri kan wata fitacciyar yar jaridar dake suka manufofin shugaba Rodrigue Duterte, wato Maria Ressa saboda samun ta da laifin wallafa rahotan da bai yiwa shugaban dadi ba.

Daya daga cikin yan jaridu a Philippines dake adawa da matakin kotun kasar
Daya daga cikin yan jaridu a Philippines dake adawa da matakin kotun kasar Reuters
Talla

Nan gaba ake saran kotun ta bayyana wa’adin daurin da aka yiwa yar jaridar wadda ta dade tana rahoto kan irin cin zarafin da jami’an tsaro keyi da sunan yaki da shan miyagun kwayoyi.

Yayin da take jawabi bayan zaman kotun, Yar jaridar tace zasu cigaba da kalubalantar masu yaki da yancin aikin jarida.

Kubgiyoyi da dama ne a Duniya suka yi Allah wadai da wannan mataki daga kotun Philippines.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI