Faransa

Litinin mai zuwa ake sa ran bude gidajen kallo a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/François Mori

A Faransa, ranar litinin mai kamawa ne ake sa ran gidajen kallo da wuraren caca za su sake bude kofofinsu bayan dakatar da duk wasu aikace –aikace sabili da cutar coronavirus .

Talla

Mako daya bayan kawo karshen batun kullen jama’a da Shugaban kasar Emmanuel Macron ya sanar,dubban yan kasar ta Faransa ke sa ran sake komawa harakokin su na yau da na kullum.

Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar a daren jiya juma’a, hukumomin Faransa sun bayyana cewa za a bude filayen wasannin kwallon kafa kama daga ranar 11 ga watan Yuli tareda baiwa yan kalo dubu biyar damar shiga wadanan wurare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.