Rasha

Shugaba Putin na fatan tsayawa shugabancin Rasha har zuwa 2030

Vladmir Putin  Shugaban kasar Rasha
Vladmir Putin Shugaban kasar Rasha Kirill KUDRYAVTSEV / AFP

Yau Alhamis yan kasar Rasha ke fara kada kuri’a a zaben amincewa da yiwa kundin tsarin mulkn kasar gyaran fuskar da zata baiwa shugaban kasa Vladimir Putin damar cigaba da zama a karagar mulki har zuwa shekarar 2036.

Talla

Jami’an gudanar da zabe sun ce fara jefa kuri’ar daga yau zai bada damar rage cin koson mutane a zaben gama gari da zai gudana ranar 1 ga watan gobe, sakamakon annobar COVID-19 wadda ke cigaba da lakume rayuka.

Shugaba Putin ya gabatar da sauye sauyen a watan Janairu wanda nan da nan Majalisar Dokoki ta amince da shi, yayin da shugaban Yan adawa Alexie Navalny ya bayyana shirin a matsayin juyin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.