Cuba-Corona-Faransa

Cuba ta aike da likitoci Tsibiri Martinique na kasar Faransa

Wasu daga cikin likitoci yan kasar ta Cuba
Wasu daga cikin likitoci yan kasar ta Cuba Domitille Piron/RFI

Kasar Cuba ta aike da kwararrun likitoci 15 da suka sauka tsibirin Martinique dake karkashin ikon Faransa don taimakawa wajen yaki da annobar Covid 19 a wannan yanki na kasar.

Talla

Jami’an kiwon lafiyar sun sauka ne daga cikin jirgin dake dauke da su,fuskoki a rufe,dauke da tutar kasar ta Cuba,za su kuma share watanni uku don ganin sun taka gaggarumar rawa a wannan yaki da cutar covid 19 da kuma tallafawa wajen karawa jami’an kiwon lafiyar tsibirin na Martinique sani a wasu fanoni daban da kuma suka jibanci kiwon lafiya.

A haka Faransa ta kasance kasa ta uku da za ta amfana da tallafin kasar Cuba ta bangaren kiwon lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI