China-Hong Kong

Amurka ta damu da kamu da ake yiwa jama'a a Hong Kong

Wasu daga cikin masu zanga-zanga da dokar China
Wasu daga cikin masu zanga-zanga da dokar China (Photo AP / Vincent Yu)

Majalisar dattijan Amurka ta kada kuri’ar amincewa da saka takunkumai kan bakuna a Hong Kong dake mu’amala da kusoshin gwamnatin China dake take hakkin masu fafutukar ganin yankin na Hong Kong ya koma kan tsarin dimokaradiya.

Talla

Matakin dai, martani ne kan sabuwar dokar tsaron kasar da gwamnatin China ta kafa kan Hong Kong, abinda manyan kasashen yammacin Turai ke kallo a matsayin hanyar kawo karshen kwarya kwaryar ‘yancin cin gashin kan da yankin ke da shi.

Fiye da mutane 300 jami’an ‘yan sandan Hong Kong suka kame ranar Laraba da ta gabata, cikinsu har da wadanda suka kalubalanci sabuwar dokar China wajen gudanar da kakkarfar zanga-zangar tunawa da zagayowar ranar da Birtaniya ta mika yankin mai kwarya-kwaryar ‘yanci ga China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.