Faransa

Shugaba Macron ya nada Jean Castex a mukamin Firaministan Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nada Jean Castex a mukamin Firaministan kasar ,yan lokuta bayan murabus na Edouard Philippe da gwamnatin kasar. 

Jean Castex sabon Firaministan Faransa
Jean Castex sabon Firaministan Faransa Ludovic MARIN / AFP
Talla

Yan lokuta da mika takardar murabus na Gwamnatin Faransa a karkashin firaminista Edouard Philippe ,Shugaban kasar Emmanuel Mcron ya nada Jean Castex a mukamin sabon firaministan kasar.

An dai haifi Jean Castex ranar 25 ga watan Yuni na shekara ta 1965 a Vic Fezensac na kasar ta Faransa.

Ana kalon sa a matsayin ma’aikaci da ya jajirce da kuma ya taka muhimiyar rawa a karkashin gwamnatoci da suka shude,kama daga Xavier Bertrand kama daga shekara ta 2006 zuwa 2007, kazalika ya na daga cikin mutanen da suka yi a karkashin gwamnatin tsohon Shugaban kasar Nicolas Sarkozy.

A ranar 2 ga watan Afrilun shekarar bana ne aka damka masa nauyin jagorantar tsarin kawo karshen batun killace mutan kasar Faransa ,tsarin da Gwamnatin kasar ta bullo da shit un bayan bulluwar cutar Coronavirus.

Sabon Firaministan Faransa Jean Castex na daga cikin jerry Faransawa da suka yi karatu a makarantar horar da kimiya siyasa dake Paris.

Jean Castex na jerryn masu ra’ayin rikau da suka goyin bayan takarar Francois Fillon a shugabancin jam’iyyar UMP a shekara ta 2012.

Jean Castex na da mata daya da ya’a hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI