Duniya

Amurka ta sanya takunkumi kan jami'an China

Kasar Amurka ta sanya takunkumi kan wasu manyan jami’an gwamnatin China kan abinda ta kira cin zarafin da suke yiwa Yan kabilar Uighur da Turkic Musulmi wadanda ke zama tsiraru a cikin kasar.

Wasu daga cikin masu kare yan kabilar Uighur a China
Wasu daga cikin masu kare yan kabilar Uighur a China KENZO TRIBOUILLARD / AFP
Talla

Amurkar tace wadannan jami’ai guda 3 da suka hada da Chen Quanguo, shugaban Jam’iyyar Kwaminisancin kasar a yankin Xijiang wanda ake zargin kitsa yadda ake azabtar da kabilun ba zasu samu damar shiga kasar ba, yayin da aka rufe kadarorin su dake cikin Amurka.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yace kasar ba zata nade hannayen ta tana ganin ana cin zarafi da kuma azabtar da Yan kabilar Uighur da Kazakhs da kuma wasu kananan kabilun dake Xinjiang ba.

Sauran jami’an sun hada da Wang Mingshan, daraktan tsaron Xijiang da Zhu Hailun, tsohon jami’in Jam’iyyar kwaminisanci dake Yankin.

Amurka ta kuma haramta duk wata hulda da ta shafi kudade da wadannan jami’ai a fadin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI