Amurka

Biden ya gabatar da shirin tattalin arzikin sa

Dan Takaran shugaban Amurka a Jam’iyyar Democrat Joe Biden ya gabatar da wani shirin sake farfado da tattalin arzikin kasar da zai ci kudin da ya kai Dalla biliyan 700, wanda ya kunshi kirkiro da sabbin ayyukan yi da kuma zuba jari a bangaren sabbin fasahohi, matakin da ake kallo a matsayin babban kalubale ga shugaba Donald Trump.

Joe Biden,dan takara a zaben shugaban Amurika daga jam'iyyar democrat
Joe Biden,dan takara a zaben shugaban Amurika daga jam'iyyar democrat ALEX WONG / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / Getty Images via AFP
Talla

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya gabatar da shirin nasa da aka yiwa lakabi da ‘Build Back Better’ ko kuma ‘sake ginawa da kyau’ wanda yayi karo da na shugaba Trump da ake kira ‘America First’.

Shirin na Biden zai taimaka wajen ceto ayyukan da akayi asarar su sakamakon annobar corona da kirkiro ayyukan yi sama da miliyan 5 wajen zuba jari a bangaren kayan da ake sarrafawa a gida da bincike da kuma kayan da ake fita da su zuwa kasashen waje.

Sabon shirin ya kunshi sake fasalin tsarin ‘Buy America’ da kara yawan haraji kan kamfanoni daga kashi 21 zuwa kashi 28 da kuma baiwa kungiyoyin ma’aikata damar karfafa ma’aikatan su.

Biden ya shaidawa ma’aikatan karafa cewar wannan ne shirin sa na sake gina Amurka bayan ya ziyarci kamfanin su mai shekaru 101 kusa da Scranton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI