Mutane da dama ne suka rasa ayyukan su a Amurka sabili da covid 19
Annobar COVID-19 ta sake raba karin mutane miliyan guda da 300,000 da ayyukan su a kasar Amurka, sakamakon cike takardun neman tallafin rasa aiki da suka gabatar a mako guda da ya gabata.
Wallafawa ranar:
Wannan ya nuna raguwar da aka samu daga miliyan guda da 44,000 da aka samu kusan kowanne mako kamar yadda hukumar kula da kwadagon kasar ta gabatar.
Masana tattalin arziki da kuma ofishin kasafin kudin Majalisa yace zai dauki shekaru kafin kasar ta koma yanayin da take kafin samun wannan annoba.
Amurkawa da dama ke ci gaba da yin Allah wadai ganin ta yada Shugaban kasar Donald Trump ke kawar da idanu tareda daukar matakai dake kawo cikas ga mutanen dake neman ayyukan yi a Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu