Wasanni

Luis Muriel na Atlanta na fama da rauni

Dan wasan gaba na Atlanta Bergame dan asalin kasar Colombia Luis Muriel da ya samu rauni a ka, yan lokuta da fitowar sa daga asibiti ya na mai bayyana cewa raunin da ya samu ba zai hana shi taka tamola da kungiyar sa Atlanta Bergame.

LUIS MURIEL dan wasan kungiyar kwallon kafar Atlanta Bergame
LUIS MURIEL dan wasan kungiyar kwallon kafar Atlanta Bergame RFI
Talla

Dan wasan gaban mai shekaru 29,ya zura kwallaye 17 da kungiyar sa a gasar Serie A. Wasu rahotanni na nuni cewa sai da likitoci suka yi masa dinky a ka.Dan wasan ya bayyana cewa tabbas a yau zai kasance a filin wasa domin nuna goyan baya ga kungiyar sa. A gobe laraba zai koma atisayi.

Wasu rahotani mabanbata daga kafofin yada labarai na nuni cewa dan wasan ya zame ne a wurin wanka.

Luis Muriel da ya fi kowane dan wasa zura kwalo a raga a gasar Serie , a karo na farko ba zai halarci wasar da kungiyar za ta yi da Lombard Brescia.

Kungiyar ta Atlanta Bergame ta samu tsallakawa zuwa gasar cin kofin zakaru na Turai,inda za ta kara da PSG ranar 12 ga watan Agusta na wannan shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI