Amurka

An sake rufe wasu gidajen abinci a California

Gwamnan jihar California dake Amurika Gavin Newsom, ya bayar da umarnin rufe wasu muhimman wuraren taruwar jama’a sakamakon tsanantar cutar Covid-19 a jihar.

Yankin California dake kasar Amurka
Yankin California dake kasar Amurka AP/Jae C. Hong
Talla

Gwamnan ya sanar da matakin ne kwana daya bayan da aka samu sama da mutane dubu 8 da suka harbu da kwayar cutar a rana daya cikin jihar ta California. Gwamnan ya sanar da daukar karin wasu matakai a cikin jihar ta California, karkashin wadannan matakai hukumomi sun bukaci illahirin gidajen abinci, na barasa, gidajen sinima da na wasan kwaikwayo da su sake rufe kofofinsu, wannan mataki ne da za a mutunta a kowane sashe na jihar ta California. Wasu daga cikin muhimman wuraren da matakin ya shafi kuwa sun hada da mujami’u, wuraren motsa jiki, manyan shaguna da kuma waruren gyaran gashi matukar dai suna a rufe da iska ma’ana dai inda iska ba ya kadawa a cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI