Taron Shugabanin Turai don ceto tattalin arzikin yankin
Shugabannin kungiyar kasashen Turai na taro a Brussels yau Juma’a game da kasafin kudi Euro biliyan 750 don tada komadan tattalin arzikinsu wanda annobar Coronavirus ya daidaita, Shugaban Bankin Turai Christine Lagarde ta ce wajibi ne kasashen su hanzarta samar da mafita .
Wallafawa ranar:
Uwargida Christine Lagarde wadda take zantawa da manema labarai kafin wannan taro na yau, tace duk da cewa harkokin yau da kullum na farfadowa ganin ana ta jingine tsauraran matakan hana walwala, batun gaggauta farfadowar tattalin arzikin kasashen na da muhimmanci.
Tace Bankin Turai yayi wasu tanade-tanade, amman kuma ana bukatar kasashen su ga lallai sun dauki matakan ganin babu jinkiri wajen murmurewar tattaln arzikin na su.
Taron na yau Jumaa da gobe asabar zai fi bada karfi ne kan asusun kudu Euro biliyan 750 da aka ware don tallafawa masashen da suka ji jiki sakamakon annobar coronavirus.
Sai dai kuma batun na fuskantar turjiya daga wasu kasashen kungiyar da suka hada da Denmark, Sweden, The Neitherlands da Austria dake bukatar ganin an bada rancen kudaden ne ga kasashen mabukata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu