Duniya

An soma zabe a Belarus

Wasu daga cikin magoya bayan yan siyasa a kasar Belarus
Wasu daga cikin magoya bayan yan siyasa a kasar Belarus G.Sharypkin/RFI

An sona kada kuri’a a zaben Shugaban kasa a Belarus, zaben da ya hada Alexander Loukachenko da ya share kusan shekaru 26 ya na shugabancin kasar da mallamar koyar da turancin ingilishi mai shekaru 37 Svetiana Tikhanovskaia.

Talla

Rahotanni daga Minsk na kasar ta Belarus na bayyana cewa jama’a sun soma isa ruhunan zabe ,a dai dai lokacin da kasashe kama daga Faransa, Jamus, Fologne suka bukaci a baiwa kowace jam’iyya damar aikewa da wakilan ta don tabbatar da sahihancin zaben.

Ana dai sa ran hukumar zabe ta fitar da sakamakon wannan zabe cikin daren gobe litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI