Amurka

Kungiyar Timbers Portland ta tsallaka gasar Concacaf

Tambarin hukumar kwallon kafar Concacaf
Tambarin hukumar kwallon kafar Concacaf

Kungiyar kwallon kafa ta Timbers ta lashe kofin arewacin Amurka na kwallon kafa bayan da ta doke Orlando da ci 2 da 1 a gasar karshe da aka fafata a jiya talata a filin wasa na Disney world dake Orlando.

Talla

Yan wasa Larrys Mabiala bafaranshe da dan Crotia Dario Zuparic na daga cikin yan wasan da suka zura kwallo a ragar Orlando, bayan mituna 27 da 66,kafin daga bisali dan kasar Uruguayen Mauricio Pereyra ya zura kwallon Orlando bayan mituna 39.

Wannan nasara na baiwa kungiyar ta Timbers Portland samun tikiti shiga jerry kungiyoyin da za a fafatawa da su a gasar Concacaf.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.