Diflomasiya

Falasdinu ta janye jakadan ta a Hadaddiyar Daular Larabawa

Wani yankin Hebron dake karkashin ikon dakarun Isra'ila
Wani yankin Hebron dake karkashin ikon dakarun Isra'ila HAZEM BADER / AFP

Hukumomin Falasdinu sun sanar da janye jakadan Falasdinawa a Hadaddiyar Daular Larabawa nan take a matsayin wani maatakin nuna rashin amincewa da maido da huldar diflomasiyya tsakanin daular da Isra’ila.

Talla

Tuni kungiyar Hamas, wacce ke iko da yankin Zirin Gaza, ta sa kafa ta shure wannan batu na danganta.

Amma shugaban Falasdinu Mahmud Abbas ya gana da jagoran Hamas, Ismail Haniyeh jim kadan bayan sanarwar maido da dangantakar duk da rashin jituwa da ke tsakaninsu.

Kasashen Lrabawa irin su Iran sun dai Allah wadai da wannan mataki da aka cimma tsakanin Isra’ila da Daular Lrabawa.

Kazzalika Firaministan Isra’ila na fuskantar suka daga cikin gida,bayan da wasu yan siyasa ke kalon sa a matsayin mutumen da ya kaucewa alkawura da ya dau dangane da batun mamayar yankunan Falesdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.