Belarus-Turai

Yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaben Belarus

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Belarus
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Belarus RFI/Gennady Sharipkin

Yar adawa ga Shugaban kasar Belarus Loukacheko ta kira yan kasar da su bijirewa sakamakon zaben dake ayana Shugaba Loukachenko a matsayin wanda ya lashe zaben kasar.Matar dake samu mafaka a Lituania,ta kira magoya bayan ta da su fito ranakun 15 da 16 na wannan wata.

Talla

Baya ga kasashen Turai da suka sanar da saka takunkunmi a jerin sunayen wasu jami’an gwamnatin Belarusse ,Hukumar UNICEF ta bayyana damuwa kan yadda yan Sanda suka yi amfani da karfin da ya wuce kima kan kananan yara a kokarin da suke murkushe masu zanga zangar adawa da shugaban kasa Alexander Lukashenko.

Wannan ya biyo bayan yadda dubban mutane a kasar suka shiga zanga zangar wadda ta kai ga kama mutane sama da 6,700 da kuma amfani da hayaki mai sa hawaye da harsashin roba.

Rahotanni sun ce jiya juma’a kungiyoyin ma’aikata sun shiga cikin jerin masu zanga zangar, yayin da kungiyar kasashen Turai ke shirin kakabawa kasar takunkumi.n

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.