Manchester United zata kara da Sevilla a gasar Europa- Ra’ayoyin ku a kai
Yau ake saran kungiyar Manchester United ta Ingila zata kara da Sevilla a gasar cin kofin Europa matakin kusa da na karshe. Shi dai wannan gasa bashi da martabar gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai wajen kudin da kungiyoyi ke samu da kuma kimar dake tattare da shi, amma samun manyan kungiyoyin dake fafatawa sannu a hankali yana daga darajar gasar.
Wallafawa ranar:
Samun damar lashe wannan kofi zai baiwa kungiyar da ta samu nasara damar shiga gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai na kaka mai zuwa kai tsaye.
Wannan karawa ta yau na da matukar tasiri ga kungiyoyin biyu, lura da cewar babu wadda ta lashe gasar league din dake gudana a cikin kasashen su.
Shin yaya kuke kallon wannan wasa zai gudana? Wacce kungiya kuke ganin zata samu nasara? Muna bukatar ra’ayoyin ku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu