Belarus-Turai

Belarus ta soke wasu daga cikin takardun izinin gudanar da aikin yan jarida

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko
Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko G.Sharypkin/RFI

Hukumomin Belarus sun soke wasu daga cikin takardun izinin gudanar da aikin yan jarida da suka baiwa manema labarai yan asalin kasashen waje dake aiki a kasar, matakin dake zuwa jajuburin gaggarumar zanga-zanga da yan adawa suka kira magoya bayan su.

Talla

Mai magana da yahun hukumar diflomasiyar kasar Anatoli Giaz, daukar matakin na biyo bayan wasu rahotanni da jami’an tsaro ke da su ,da kuma ke nuna cewa yi haka zai fi dacewa don yaki da tsageranci da kuma ta’addanci a kasar ta Belarus.

Shugaban kasar Alexander Loukachenko dake kan karagar mulki tun a shekara ta 1994,da kuma hukumar zabe ta sake ayana shi a matsayin mutumen da ya lashe zaben da ya gabata na ranar 9 ga watan agusta , na fuskantar bore daga bangaren yan adawa dake bukatar ganin ya sauka daga wannan mukami na sa.

Rasha ta bayyana cewa ta na a shirye don kai dauki ga kasar Belarus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.