Turai-Coronavirus

Yan Sandan Jamus sun tarwatsa masu zanga-zanga a Berlin

Masu zanga-zanga a Baline na kasar Jamus
Masu zanga-zanga a Baline na kasar Jamus REUTERS/Axel Schmidt

Yan Sanda a Jamus sun tarwatsa masu zanga-zanga dake adawa da matakin sanya kyalen rufe hantsi da baki a Baline na kasar ta Jamus.Yayinda aka bayyana cewa kusan mutane 38.000 ne suka halara a wannan ganggami, hukumomin birnin sun bayyana damuwa matuka ganin rashin bin dokokin kariya daga masu zanga-zanga a wannan lokaci da cutar Covid 19 ke ci gaba da barna.

Talla

Wasu kungiyoyi a kasar ta Jamus na dada nuna rashin gamsuwar su dangane da wannan mataki da yan sanda suka dau na neman dakatar da taron ga baki daya.

Masu zanga-zangar na ta fadar cewa Merkel ki yi murabis.

Kazzalika a wasu biranen Turai ,kama daga Paris, Landan ne aka gudanar da irin wanan zanga-zanga ta nuna adawa dangane da matakan tsauri da hukumomin wadanan kasashe suka dauka wajen yakar covid 19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.