Turai

An cafke wani hafsan sojin Faransa dake yiwa Rasha aiki

Florence Parly, Ministan tsaron Faransa
Florence Parly, Ministan tsaron Faransa © RFI

A Faransa, jami’an dake sa ido kan ayukan leken asiri sun capke wani hafsan sojan kasar da ake zargi da tseguntawa rasha da wasu bayyanai sirri.

Talla

Ministan tsaron kasar Faransa Florence Parly ta sanar da dakatar da wani babban hafsan sojin kasar dake aiki a cibiyar tsaro ta Nato dake Italiya bisa samun sa da laifin tseguntawa Rasha da wasu bayanan sirri. Jami’an dake sa ido kan ayukan leken asiri Faransa ne suka kama shi bayan ya mika wasu bayanai ga jami’an Rasha.

Da sanyi safiyar jiya lahadi ne gidan rediyo Europe 1 dake Faransa ya sanar da kama hafsan sojan kasar bayan gano cewa ya na baiwa Rasha wasu bayanan siri.

An dai kam shi a lokacin da yake kokarin komawa Italiya bayan gajeren hutu da ya samu,ya kuma dawo kasar sa Faransa, ya na dai tsare yanzu haka a wani kurkuku dake Paris.Tun ranar 22 ga watan yuli ne masu bincike suka mayar da hankali a kan sa,bisa zargin sa da cin amana,wanda kuma doka ta hukunta masu aikata irin wannan kuskure.

Ministan tsaron kasar ta Faransa Florence Parly ta ce hukumomin Faransa za su bayar da hadin kai don ganin gaskiya ta bayyana dangane da wannan bincike har indan ta kama hukunta duk masu hannu a wannan tafiya.

A watan yuli da ya gabata ,masu yaki da falasa bayan siri sun capke wasu ma’aikata biyu da ake tuhuma da tseguntawa China da wasu bayyanan sirri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.