Gabas ta tsakiya

Isra'ila na tattaunawar sirri da wasu manyan kasashen larabawa

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu Menahem Kahana/Pool via REUTERS

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi ikirarin cewa yanzu haka yana tattaunawar sirri da wasu manyan kasashen larabawa don kulla huldar Diflomasiyya dai dai lokacin da jirgin kasuwanci na farko ke tashi daga Tel Aviv zuwa Dubai, bayan dawowar alakar Diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Talla

A ranar 13 ga watan nan ne dai Amurka ta shige gaba wajen gyara alakar Diflomasiyya tsakanin Isra’ilan da hadaddiyar Daular Larabawa, kasar da ta zamo ta uku a yankin gabas ta tsakiya bayan Masar da Jordan da ta kulla alaka tsakaninta da kasar ta Yahudawa da musulmi ke kallo a matsayin haramtacciya.

A cewar Netanyahu yana da kwarin gwiwar gyaruwar alaka tsakanin kasashen na Larabawa da Isra’ila, bayanda Daular ta larabawa ta fara bude musu hanya a baya-bayan nan, dai dai lokacin da yau litinin jigin ‘yan kasuwa dauke da fasinja ke tasowa daga Tel Aviv zuwa Dubai.

Yayin taron kaddamar da fara jigilar jiragen daga Isra’ila zuwa Dubai a jiya Lahadi bisa jagorancin Netanyahu da tawagar wakilan Amurka karkashin jagorancin Jared Kushner Firaministan ya bayyana yadda bangarorin biyu ke tattaunawar yiwuwar kulla yarjejeniyar tsaro kasuwanci da kuma sufuri baya ga yawon bude ido da za su fara aiki nan gaba kadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.