Amurka

Melania Trump ta kare Donald Trump

Melania Trump mai dakin shugaban Amurka Donald Trump
Melania Trump mai dakin shugaban Amurka Donald Trump Alex Wong/Getty Images/AFP

Melania Trumps uwargindan Shugaban Amurka Donald Trump a jiya juma’a ta yi kokarin kare mijin ta ganin caccaka da yake ci gaba da fuskanta biyo bayan wasu kalamai da ya furta a yayinda ya ziyarci Faransa a shekara ta 2018.

Talla

A lokacin ziyarar, shugaba Trump ya bayyana cewa ba zai ziyarci makabarta da aka bine sojojin Amurka shekara 100 bayan yakin Duniya na farko,inda shugaban na Amurka a cewar majiya ya bayyana cewa mai nene alfanun ziyarar ta sa a wannan makabarta da aka bine marar nasara.

Wata mujala da aka sanni da The Atlantic ce ta sake dawo da labarin ,da yanzu haka akasarin Amurkawa ke ta bayyana furucin a kai.

Shugaba Trump kamar dai yada ya saba ya aike da sako ta twitter da cewa, mujalar da ta kama hanyar rushewa,ya zama dole ta dinga kakkalo labaren da ba su da tushe da nufin ba ta mini suna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.