Amurka

Kasashen Duniya sun soki ikirarin shugaba Trump ga magoya bayan sa

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Leah Millis

Wasu kasashen Duniya sun soma bayyana damuwa biyo bayan gayatar shugaban Amurka ga magoya bayan sa cewa su kada kuri’a sau biyu.Daga cikin wadanan kasashe,Jamus na sahun gaba, inda kamar dai yada shugaban diflomasiyar kasar Helko Maas a wata zantawa da wata mujalar kasar ya bayyana cewa lalle abin da ban mamaki a ce kasa kamar Amurka, kuma shugaban dan takara ya fito fili ya na gayatar jama’a da su kada kuri’a sau biyu.

Talla

Jami’in diflomasiyar ya na mai cewa,ya na da yekinin Shugaba kuma dan takara Donald Trump zai gujewa duk abubuwan da za su iya janyo yammuci a zaben Amurka.

Sai dai kamar yada Donald Trump ya saba,ya mayar da martani tareda aikewa da sako ta kaffar twitter cewa, inda tsarin su ya fi nasu inganci,to babu ta yada za su je zabe sau biyu.

Tun a jiya asabar aka soma kada kuri’a ta hanyar Email a wasu yankunan Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.