Gabas ta tsakiya

An sake samun gobara a tashen jiragen ruwan Beirut

Yadda gobarar  ta ratsa tashar jiragen ruwan Beirut
Yadda gobarar ta ratsa tashar jiragen ruwan Beirut AP Photo/Hussein Malla

An sake samun tashin gobara a tashen jiragen ruwan birnin Beirut na kasar Libanan, a daidai lokacin da mahukunta ke ci gaba da gudanar da binciken musabbabin fashewar da ta faru a tashar sama da wata daya da ya gabata.Bayanai sun ce gobarar ta kone babban rumbun adana kayayyakin agajin wucin gadin da aka samar a baya bayan nan.

Talla

Masu bincike sun kasa gano dalilin tashin wannan sabuwar gobara, wadda ta faru a dai-dai lokacin da al’ummar kasar ke ci gaba da juyayin mutuwar mutane 192 da kuma raunata wasu dubu 6 da 500 a ranar 4 ga watan agustan da ya gabata.

A wannan karo dai gobarar ta tashi ne a sashen da ake ajiye tayoyi da kuma man da ake sanya wa motoci, to sai dai bayan mintuna kadan da tashin gobarar, jami’an kwana-kwana sun yi nasarar kashe wutar tare da takaita illolinta.

Samun labarin tashin wannan gobara karo na biyu, lamari ne da ya yi matukar tayar da hankulan ma’aikata a tashar jiragen ruwan.

An ga mutane na gudu suna barin tashar jiragen ruwan na birnin Beirut, yayin da masu ababan hawa ke gaggawar nisantar da kansu daga unguwar. To sai dai nan take mahukunta suka tura dimbin sojoji domin fara ayyukan ceto tare da taimakawa don kashe gobarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.