Turai

An rantsar da Alexander Loukashenko a asirce

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko
Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko REUTERS/Vasily Fedosenko

A yau laraba aka rantsar da Shugaba Alexander Lukashenko a asirce a Minsk dake babban birnin kasar Belarus, karo na 6 , bayan da ya ayyana kansa da cewa shine ya lashe zaben kasar da ‘yan adawa ke ci gaba da bore saboda tsaban rinto da suke zargin anyi.

Talla

Kasashen Turai da dama sunki amince da Lukashenko musamman Jamus, yayinda Kunigiyar Tarayyar Turai ke shirin kirbawa Belarus takunkumin kariya tattalin arzikin.

Uwargida Svetlana Tikhanovskaya ‘jagorar yan adawa da ta ke cewa ita ta lashe zaben ta nemi kasashen duniya da kada su amince da zaben Lukashenko.

Shugaban na Belarus dake samun goyan bayan Shugaban Rasha Vladmir Poutine ya tsaya kai da fata cewa babu ta yada zai mika iko ga masu kokarin durkkusar da kasar Belarus tareda hada baki da wasu kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.