Turai

Za a komawa fagen Ligue 1 a Faransa

Wasu daga cikin magoya bayan kungiyar kwallon kafar  Lyon ta kasar Faransa
Wasu daga cikin magoya bayan kungiyar kwallon kafar Lyon ta kasar Faransa REUTERS/Gonzalo Fuentes

A gobe asabar ne St Etienne da Rennes za su ketse reni a kokarin kowanen su na neman matsayi na farko a gasar Ligue 1 ta kasar Faransa.Yanzu haka dai kowane daga cikin wadanan kungiyoyi na da maki 10.Fafatawar ta gobe dai ba za a baiwa yan kalo damar shiga filin wasa sabili da cutar Coronavirus dake ci gaba da halaka rayukan jama’a.

Talla

Kalo ya koma a daya Geffen zuwa kungiyar PSG da za ta fafata da kulob na Reims ranar lahadi.

Wanan dai ne karo na farko tun ficewar kungiyar ta PSG a gasar cin kofin zakaru da ake sa ran zata gabatar da yan wasan ta,ko mu ce za ta kure adaka.

Yan wasa biyu dai ne yanzu haka a kungiyar ta PSG da ba za su kasance a fili ba da suka hada da Juan Bernat da ya samu rauni da kuma zai kauracewa filin wasan a tsawon watani sai Layvin Kurzawa da aka dakatar a matsayin hukunci bayan wasar da kungiyar PSG ta yi da Marseille.

Ana sa ran mai horar da kungiyar ta PSG zai baiwa yan wasa da suka hada da Mbappe,Neymar,Mauro Icardi da Angel Di Maria a wannan fafatawa da Reims.

Ga dai yada za ta kaya a wannan gasar Ligue 1 ta kasar Faransa:

A yau Lille- Nantes sai gobe indan Allah ya kai mu

Sait Etienne-Rennes.

Marseille-Metz.

Ranar Lahadi

Bordeaux- Nice.

Nimes- Lens.

Monaco - Strasbourg.

Dijon –Montpellier.

Angers - Brest.

Lorient -Lyon, sai PSG Reims ranar Lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.