Faransa-Lebanon

Shugaba Macron ya zargi yan siyasar Lebanon da cin amana

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a Beirut na kasar Lebanon
Shugaban Faransa Emmanuel Macron a Beirut na kasar Lebanon Lewis Joly / AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya zargi shugabannin siyasar Lebanon da cin amana wajen gazawa su kafa gwamnatin da zata tinkari matsalolin da suka addabi kasar bayan iftila’in da ya afkawa kasar.

Talla

Yayin jawabi ga manema labarai kan rikicin Lebanon, Macron yace shugabannin siyasar sun ci amanar jama’ar kasar bayan alkawarin da suka dauka, inda ya bayyana matakin a matsayin abin kunya.

Shugaban Faransa yace ‘yan siyasar sun fi fifita bukatun sun kan su maimakon makomar kasar wadda ke fuskantar dimbin matsalolin dake mata barazana.

Macron ya kuma gargadi kungiyar Hezbollah dake samun goyan bayan Iran da hannu wajen matsalar da aka samu, inda ya bukace ta da ta mutunta jama’ar kasar.

Sau biyu shugaba Macron ke ziyarar Lebanon bayan hadarin da aka samu a tashar jiragen ruwan kasar, inda ya jagoranci kaddamar da gidauniyar tallafawa jama’ar kasar da kudade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.