Turai-EU

Birtaniya ta shirya don kama gaban kan ta daga tattaunawa da Turai

Firaministan Birtaniya Boris Johnson
Firaministan Birtaniya Boris Johnson REUTERS/Toby Melville/Pool

Firaministan Birtaniya Boris Johnson yace a shirye suke su kama gaban kan su daga tattaunawar da ake domin kulla yarjejeniyar kasuwancin da Turai, muddin ba’a gudanar da gagarumar sauyi kan abinda kungiyar ke bukata ba.

Talla

Yayin da yake tsokaci kan matsayin shugabannin Turan dake taro a Brussels, Johnson yace ba zasu bada kai bori ya hau ba wajen kare muradun su.

Tarayyar Turai ta ce kimar Birtaniya na fuskantar barazanar zubewa a daidai lokacin da bagarorin biyu ke kokarin warware dangantakar kasuwanci da ke tsakaninsu tsawon shakaru 50 biyo bayan wata kuri’ar jin ra’ayi da ta raba kan al’ummar kasar.

Tarayyar Turai ta yi watsi da ikirarin da firamistan Birtaniya Boris Johnson ya yi cewa tana kitsa manakisar wargaza kasarsa, a yayin da aka shiga wani makon da za a ci gaba da tattaunawa mai sarkakiya don cimma yarjejeniya kan yadda kasuwanci zai kasance bayan rabuwa.

Yakin cacar baki tsakanin bangarorin biyu ya kazanta ne sakamakon wani sabon kudirin da Johnson ya gabatar, wanda Birtaniyar da kanta ta ce lallai ya saba wa tanade-tanaden yarjejeniyar yin hannun riga ta Turai, lamarin da ya janyo martani cikin fushi daga tsaffin firamistocin kasar Tony Blair da John Major, da ma ‘yan majalisar dokokin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.