Isa ga babban shafi
Faransa

An file kan malamin tarihi a Faransa

Yankin Conflans da aka sare kan malamin tarihi
Yankin Conflans da aka sare kan malamin tarihi REUTERS/Charles Platiau
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

Jami’an tsaro a Faransa sun danganta maharin da ya sarewa wani malamin tarihin kasar faransa kai a yau juma’a a garin conflans-Saint-Honorine, dake ajen birnin paris, da zama mai tsatsauran ra a yin musulunci, sakamakon kabarar da ya yi kafin jami’an tsaro su harbe shi.

Talla

Wannan malami da ya nunawa daliban sa wani zane da ake dangantawa da mai tsira alait wasalam ya rasu bayan da wani mutum ya kai masa hari tareda file masa kai.

Mutuwar malamin na zuwa ne makonni uku bayan da wani dan kasar Pakistan ya kai harin daf da cibiyar mujalar Charlie Hebdo.

Daga masu bincike maharin ya aikata kisan malamin tarihin ne kusa da makaranatr da yake koyarwa dake Confians Sainte Honorine.

Nan take kotu mai shigar da karar gwamnatin kan ayukan ta’addanci ta kasar ka kaddamar da bincike a kai,da samun labarin Shugaban kasar Emmanuel Macron da ake sa ran zai kai ziyara unguwar da aka kai harin ,ya ziyarci cibiyar yaki da ayukan ta’addanci dake ofishin Ministan cikin gidan kasar ta Faransa.

Ministan cikin gidan kasar dake ziyara Morocco ya yake ballugoro,ya kuma kama hanayr dawowwa gida.

Ta bakin yan Sanda an kai wa malamin hari ne da misalin karfe biyar na yaman nan ,

Yan Sanda da aka kira sun samu nasarar kashe maharin,wanda bayan kisan mallami,ya yi barrazanar afkawa jami’an tsaro,wanda suka kuma hallaka shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.