Wasanni-Kwallon kafa

Za a komawa fagen Ligue 1 a Faransa

Wasu daga cikin magoya bayan PSG a Faransa
Wasu daga cikin magoya bayan PSG a Faransa GEOFFROY VAN DER HASSELT / AFP

Bayan share wani gajeren lokaci ba tareda an gudanar da gasar Ligue 1 a Faransa, a yau juma’a wasu daga cikin kungiyoyin kasar za su koma fagen tamola a mataki na bakwai.PSG za ta yi tattaki zuwa Nimes inda za ta kara da kulob na Nimes, yayinda Rennes za ta bakuci Dijon a yau dinan.

Talla

A gobe indan Allah ya kai mu akwai wasa tsakanin Reims da Lorient, Bordeaux za ta bakuci Marseille sai ranar Lahadi Strasbourg Lyon, Angers-Metz, Monaco Montpellier.

Nantes –Brest, St Etienne Nice ka na Lille Lens.

A jadawalin gasar ta Ligue 1.

Rennes ke mataki na farko da maki 14.

Lille a matsayi na biyu da maki 14,Lens ta uku da maki 13, PSG a mataki na hudu da maki12 sai Montpellier a mataki na biyar da maki 10.

A yau juma’a hukumar kwallon kafar yankin Asiya ta bayyana cewa yanzu haka komi ya kankama,dangane da kasar da za ta dau nauyin shirya wasar karshe na cin kofin zakarun na yankin Asiya.

Bayan da aka share dogon lokacin ana ta dage lokaci,hukumar ta fitar da sunan kasar Qatar,magatakarda na hukumar kwallonkafar Asiya Windsor John ne ya sanar da haka a yau juma’a,wannan gasa na daya daga cikin wasani dake kayatar da jama’a a wannan yanki na Asiya.

A watan Maris na wannan shekara ne aka dakatar da duk wasu wasanni sabili da cutar Corona,kazalika kasar ta Qatar ce za ta karbi bakucin gasar cin kofin Duniya na shekara ta 2022.

Kungiyoyi a yammaci da suka fafata a tsakanin su,an samu kungiyar Persepolis da ta samu tsallakawa mataki nag aba a fafatawa da ta yi da Al Nasr.

A gabaci ,inda akeda kungiyoyi da suka hada da Japon,China da Austria,wadanan kungiyoyi za su fafata tsakanin su kama daga 18 ga watan Nuwamba zuwa 13 ga watan Disemba na wannan shekara.

Hukumar ta dau mataki da ya kai ta ga dakatar da kungiyar Al Hilal wace aka sama da laifin jera yan wasa kalilan bayan da aka gano cewa da dama daga cikin yan wasan kungiyar sun kamu da cutar Coronnavirus.

Yan sanda a kasar Tcheque sun cafke akalla mutane 19 da ake tuhuma da hannu dumu-dumu a zantukan da suka jibanci cin hantsi da asasa rashawa yayin wasannin kwallon kafa.

DaMichal Jurman mai magana da sunan hukumar kwallon kafar kasar ne ya fitar da wannan labari a yau,inda ya karasa da cewa hukumar dake yaki da rashawa ta kasar ce ta aiko da wakilan da suka dirawa jami’an a lokacin da suke wata ganawa a cibiyar hukumar kwallon kafar kasa dake birnin Prague.

Majiya daga wasu kaffafen yada labarai na nuni cewa daga cikin muatanen da ake tsare da su ,sun hada da mataimakin shugaban hukumar kwallon kafar kasar dake rike da wannan mukami tun a shekara ta 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.