Iran-Amurka

Duk kasar da ta kuskura sayarwa Iran makamai, zata fuskanci matakin ladabtarwa -Pompeo

Wasu daga cikin makamai da Iran ke fatan sayarwa kasashen Duniya
Wasu daga cikin makamai da Iran ke fatan sayarwa kasashen Duniya WANA (West Asia News Agency) via REUTERS

A shirye Amruka take ta yi amfani da ikon cikin gida da take da shi, wajen daukar matakin ladabtarwa kan duk wani mutum ko kasar da ta bada gudummawa dakon makaman, sayar da su ko kuma isar da manyan makaman kaifi ga kasar Iran. In ji sakataren harakokin wajen Amruka Mike Pompeo.

Talla

Pompeo ya kara da cewa, duk kasar dake kaunar zaman lafiya ya tabbatu a yankin gabas ta tsakiya to kuwa kamata ya yi ta kauracewa kulla kasuwancin makamai da kasar Iran.

Yarjejeniya da kasashen duniya suka cimma kan aikin yinkurin samar da makamashin nukliyar kasar Iran a 2015. Cewa ta yi, duk wani takunkumin hana sayarwa iran makamai da majalisar dinkin duniya ta kakaba mata zai daina aiki ne jiya lahadi 18 ga watan octoba 2020.

Amuruka da ta fice daga yarjejiniya nukliyar shekaru 3 da saka mata hannu, ta cimma rashin nasara a yinkurin da ta yi na son ganin komitin tsaro na MDD ya tsawaita wa’adin takunkumin kan kasar ta Iran

A ranar  lahadi da ta gabata ne Tehran ta bayyana cikar wa’adin kamar yadda yarjejeniyar da kasashen duniya suka cimma da Iran ta tanada , wa adin takunkumin ya cika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.