Lebanon

Michel Aoun ya nada Saad Hariri a mukamin Firaminista

Saad Hariri Firaministan Lebanon
Saad Hariri Firaministan Lebanon REUTERS

Shugaban kasar Lebanon Michel Aoun  ya nada tsohon Firaminista Saad Hariri a matsayin sabon Firaministan domin kafa gwamnatin da za ta jagoranci sake gina kasar da kuma shawo kan matsalar tattalin arzikin ta.

Talla

Hariri zai sake rike mukamin ne shekara guda bayan saukar sa a kai sakamakon matsin lamba daga masu zanga zangar da suka nemi sake fasalin siyasar kasar.

Kasar Lebanon na fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya wajen ganin ta kafa gwamnati, yayin da sabon Firaministan Hariri ya sha alwashin nada kwararrun mutane kamar yadda shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukata.

Sabon Firaministan ya sha alwashin kafa gwamnatin cikin lokaci ganin yadda lokaci ke kurewa, kuma daga juma’ar nan zai fara tintibar mutanen da suka kamata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.