Turai-EU

Tarrayar Turai da Birtaniya sun kakabawa wasu jami’an Rasha takunkumi

Ministan tsaron Rasha tareda Shugaban leken asirin kasar Igor Kostyukov
Ministan tsaron Rasha tareda Shugaban leken asirin kasar Igor Kostyukov Russian Defence Ministry/Handout via REUTERS

Kungiyar Kasashen Turai da Birtaniya sun kakabawa manyan jami’an liken asirin Rasha takunkumi saboda hannun da suke da shi wajen kutsen da suka yiwa Majalisar dokokin Jamus ta hanyar komfuta a shekarar 2015.

Talla

Abaya dangantaka ta yi tsami tsakanin Jamus da Rasha sabili da sakawa dan adawan Rasha guba.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce ana iya samun matsala a aikin shimfida bututun iskar gas na Nord Stream 2 idan Rasha ta gaza gudanar da bincike a game da shayar da jagoran ‘yan adawan kasar, Alexei Navalny guba.

Takunkumi da Birtania da Tarrayar Turai suka sanar ya shafi shugaban hukumar leken asiri Igor Kostyukov da Dmitri Badin wadanda aka haramtawa sanya kafa a nahiyar Turai da kuma rufe asusun ajiyar su.

Ita ma Birtaniya wadda ta janye daga kungiyar Turai a watan Janairu tace zata bi sahun kungiyae wajen aiwatar da takunkumin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.