Amurka-Zabe

Trump da Biden sun yi ta sukar juna kan cin hanci da korona

Donald Trump da Joe Biden a lokacin muhawara ta karshe
Donald Trump da Joe Biden a lokacin muhawara ta karshe Chip Somodevilla/Pool via AP

Shugaban Amurka Donald Trump da abokin karawar sa Joe Biden sun yi ta sukar juna kan cin hanci da annobar korona aa mhawara ta karshe da suka tafka kwanaki 12 kafin gudanar da zaben kasar.

Talla

Trump ya zargi ‘dan Biden Hunter da cin hanci a kasashen Ukraine da China, yayin da Biden ya zargi shi da salwantar da rayukan Amurka sama da 220,000 sakamakon cutar korona.

Tsohon Mataimakin shugaban kasa Joe Biden kuma dan takarar Jam’iyyar Democrat Joe Biden ya zargi shugaba Donald Trump da kin biyan haraji da kasa kare rayukan Amurkawa daga annobar korona da kuma kawance da dan banga Kim Jong Un shugaban Koriya ta Arewa.

Biden wanda ya sha alwashin samar da miliyoyin ayyukan yi, yace zai dawo da kima da mutuncin Amurka a ciki da wajen kasar.

Shugaban Amurka kuma dan takara Donald Trump ya bayyana cewa ya na da alkaluma dake nuna masa adadin bakaken fata marasa aikin yi mafi karanci a tarihin Amurka da mutanen Hisania da mata da mutanen Asia, mutane masu kwarewa da marasa kwarewa, wadanda suka kamala karatun MIT na farko a aji, kowanne na da adadi mai kyau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.